Na Bata Goma Hausa Novel Complete
Na Bata Goma Hausa Novel Complete *NA ƁATA GOMA….!* *5STARS EXPENSIVE COMPANY* *RUBUTAWA; MARYAM IBRAHIM (DOCTOR MARYAMAH)* *Bisimillahir Rahmanir Rahim* *Shafi na farko.* ‘Matsanancin laushin dake ƙara ratsa dukkan sassan jikina shi ne ummul’aba’isan ƙara lafewata, tare da ƙara baje jiki ina jan bargo kan jikina. Shi ma bargon sanyi haɗi da laushi na musamman na ƙara jin ya yi, cike da zallar shauƙi na ke ƙoƙarin miƙa hannuna domin in lalaubo Auta inji wanne sashe ta ke, dama ne ko hagu? Kasancewar ina ɓararrake ne a tsakiyar gadon. Ƙusa ƙusa, laushi laushi, cike da tauri taurin abu su ne suka yiwa hannu na maraba da sauka, cike da azama na buɗe idanuwana, sai dai kaf ɗakin ba zaka samu ganin ko da tafin hannunka ba ne a ciki, saboda tsabar duhun da ya mamaye ɗakin. Miƙa hannuna na yi ƙarƙashin pillow da zummar ɗauko fitila, sai dai wayam! Bata gun da ...