Ladubban Daren Farko Ga Ma'aurata
Ladubban Daren Farko Ga Ma’aurata MATASA DA YAN MATAN WANNAN ZAMANIN SAI MU GYARA GASKIYA Da ango ya shigo dakin sabuwar amaryarsa, bayan ya zauna, sai ya yi mata sallama cikakkiya, watau: ‘Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh,’ Ita ma sai ta amsa da irin haka, watau: ‘wa alaikumus salamu wa rahmatullahi wabarakatuh.’ Yadda Amarya Zatayi a Daren Farko Ya fi kyau ya hada da mika mata hannu su yi musabaha tare da sallamar. Sannan sai ya aza hannunsa na dama bisa saman goshin amaryarsa ya karanta wannan addu’ar: ‘Allahumma Inniy as’aluka khayraha wa khayra ma jabaltaha alayhi, wa a’uzu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alayhi.’ Ita ma Amarya sai ta dora hannunta saman goshin angonta ta karanta kamar haka: ‘Allahumma inniy as’aluka khayrahu wa khayra ma jabaltahu alayhi, wa a’uzu bika min sharrihi wa sharri ma jabaltahu alayh.’ To daga nan sai su yo alwalla su yi sallar na...