Cousins Ne Hausa Novel Complete
Cousins Ne Hausa Novel Complete COUSINS NE *NA NANAHKHADII* Page… 1&2 Yanayi ne na sanyi, duk wata bishiya kad’awa takeyi, hakkan yasa garin yayi d’ad’i, da wannan lokaci na bazara, hakanne yasa duk wani Dan adam, dake cikin garin sanye yake, da kayan d’ari…. Sharad’a phase 2 kenan, unguwa ce ta masu Hali, hakanne yasa ko ishasshen motsi babu, ba wani tafiya nayi ba na hanga, wani k’aton gidan sama mai farin Gate, koda nashi ga d’akin dana ji motsi na kutsa kai, kwance take kanta ko d’an kwalli babu, ta duk bak’in gashinta ya bazu a pillown da take kwance, duk hankalinta nakan instagram d’in da take kallo, hakanne yasa bata maji fitowan, Fateemeerh daga toilet ba, da haryanzu jikinta ke turiri,alaman ruwan datayi wanka dashi yana da zafi sosai, k’arasawa tayi tare da yarfa mata ruwan dake hannunta, sai time d’in ta d’a...